Labarai
Kamfanin NNPC ya tallafawa asibitin Aminu Kano
Kamfanin mai na kasa NNPC ya baiwa Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano sabbin na’urorin dashen koda, zuciya, Hunhu da kuma hanji domin rage yawan ‘yan Nigeria dake zuwa kasashen ketare don yin dashen.
Karamin Ministan Mai nasa kasa Mele Kyari ne ya bayyana hakan a yau lokacin bikin kaddamar da sabbin kayayyakin dashen koda da zuciya da Kamfanin mai na kasa NNPC ya baiwa Asibitin koyarwa na Aminu Kano.
Mele Kyari wanda ya samu wakilcin Alhaji Abubakar Nuhu Muhammad ya ce sun dauki matakin ne domin takaita kwararar al’ummar Najeriya zuwa kasashen waje domin neman magani, inda ya ce hakan zai rage yawan kudin da ‘yan Najeriya ke kashewa a kasashen waje.
Abubakar Nuhu ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su rika tallafawa bangaren lafiya domin ceto rayukan masu karamin karfi.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa mutane da dama ne suka halarci taron kaddamar da sabbin kayayyakin da kamfanin NNPC ya baiwa Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano domin tallafawa al’umma baki daya.
You must be logged in to post a comment Login