Labarai
Kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya sun yi barazanar dakatar da ayyukansu

Kamfanonin samar da wutar lantarki a fadin Najeriya nan sun yi barazanar dakatar da ayyukansu na samar da wuta saboda tarin bashin da ya haura sama da naira tiriliyan 5, da har yanzu gwamnati ba ta biya su ba, wanda ke barazana ga cigaban aikinsu na samar da lantarki a ƙasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Shugabar ƙungiyar kamfanonin samar da lantarkin, Dakta Joy Ogaji, ta bayyana cewa kamfanonin sun jima suna nuna kishin kasa ta hanyar ci gaba da samar da wuta duk da rashin biyan su kuɗaɗensu, amma yanzu sun gaji.
Ta ce, akwai sabon bashi da ya kai sama da naira tiriliyan 1, daga wutar da aka samar a farkon rabin shekarar 2025, wanda ya ƙaru kan bashin da suke bin gwamnati zuwa naira tiriliyan sama da 5.
A cewarta, Kuɗin da ake kashewa wajen samar da wuta a kowane wata yana kai wa naira biliyan 250, amma gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 900 kacal a kasafin kuɗin 2025, kuma har zuwa yau ba a samu cikakken tabbacin samun wannan kuɗi ba.
You must be logged in to post a comment Login