Connect with us

Labarai

 Sojoji 292 ne za su rubuta jarrabawar karin girma

Published

on

Akalla jami’an soji 292 ne za su rubuta jarrabawar karin girma ta manyan jami’ai.

Jarrabawar wadda za a gudanar a cibiyar horas da jami’an soji na Infantry dake Jaji a jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce jarrabawar za ‘a dauki tsawon mako daya ana gudanar da da jarrabawar

Shugaban makarantar, Manjo Janar Lucky Irabor ne ya bayyana hakan, yayin da yake yiwa manema labarai a jiya Lahadi.

Manjo Janar Irabor ya bukaci jami’an da su mai da hankali don ganin sun samu sakamako mai kyau, kasancewar za a yi amfani da shi wajen kara musu girma.

Manjo Janar Lucky Irabor ya kuma gargade su da, su kaucewa mummunar ta’adar nan ta satar amsa a ya yin rubutu jarrabawar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!