Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Ƴan bindigar da jama’a suka kama a unguwar Yamadawa suna hannun mu – ƴan sanda

Published

on

Rundunar ‘ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wasu mutane biyu da ake zargin ƴan fashi da makami ne a unguwar Yamadawa dake karamar hukumar Gwale a jiya Laraba.

A cewar mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta cikin wata sanarwa da ya fitar ya kuma rabawa manema labarai da yammacin yau Alhamis, an kama mutanen ne lokacin da su ke yunkurin yin fashi da makami a unguwar ta Yamadawa.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce da misalin karfe sha daya na daren jiya Laraba ne suka samu rahoton ƴan fashin a ungwar Yamadama wadanda suka tare wani mutum a kofar gidansa za su kwace masa mota kuma ana tsaka da hakan ne suka jiyo harbin bindiga.

Ya ce an samu nasarar kama mutanen ne sakamakon hadin kan jami’an ƴan kungiyar sintiri ta Vigilante da al’ummar gari, inda suka yi musu tara – tara sannan suka kama biyu daga ciki, wadanda suka hada da: Abdullahi Isma’il mazaunin unguwar Sani Mainagge da Abubakar Hussain Kankiya dan asalin jihar Katsina wanda tuni ya riga mu gidan gaskiya sakamakon duka da jama’a su ka yi masa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!