Labarai
Kano: Ƴan sanda sun cafke matashin da ya yi yunƙurin kashe kansa

Rundunar yan sandan jihar kano ta tabbatar da cafke wani matashi da ake zargi da yunkurin kashe kansa ta hanyar hawa saman wani dogon karfe da ke kusa da Gadar Lado bayan ya shafe tsawon tafiyar kafa daga jihar Lagos domin ganin wani mawaki.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan SP A abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Faifan bidiyon ya nuna yadda Kiyawa ke yin tambayoyi ga matashin da ake zargi mai suna Dikko Jibril dan asalin jihar Katsina.
SP kiyawa ya kuma ce, da zarar an kammala bincike kan wanda ake zargin, za su gurfanar da shi a gaban kotu domin daukar mataki na gaba.
You must be logged in to post a comment Login