Labarai
Kano : Akwai karancin bandakunan bahaya
Mataimakin daraktan tsafta a ma’aikatar muhalli da ke nan Jihar Kano lbrahim Nasir ya ce, rashin wadatattun bandakuna ko wurarren bahaya na daya daga cikin abubuwan dake ci haddasa cututtuka tsakanin al’umma.
Malam Ibrahim Nasir ya bayyana hakan ne a wani bangare na bikin ranar Bandakuna ta Duniya wanda ake gudanarwa a yau.
Ya kara da cewa, a wasu lokutan rashin bandakuna na sa wasu al’umma yin bahaya a sarari, wanda hakan ke hadasa cututtuka irin su Amai da gudawa da dai sauran su,
Dokar tsaftacce soshiyal midiya ba zata yi tasiri ba – Aminu Mai dawa
Ganduje ya rantsar da kwamishinoni ranar tantancewa
Jihar Kano ce kan gaba wajen gurbatar muhalli- Airvisual
Majalisar dinkin duniya ce ta keba duk ranar sha-tara ga watan Nuwambar kowace shekara a matsayin ranar Bandakuna ta Duniya.
Ku saurari labaran mu na Freedom don jin cikakken rahoto kan wannan ranar