Labarai
Kano: An samu tashin Gobara a gidan Mai na Al-Ihsan da ke Sharada

A daran ranar Alhamis din makon nan ne Gobara ta tashin a gidan Mai na Al-Ihsan da ke kan titin Sharada, a Kano.
Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 11:00 zuwa 12:00 na dare a daidai lokacin da ake tsaka da sauke man Fetur.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, jami’an hukumar kashe gobara sun isa wurin domin dakile yaduwar wutar, inda kuma ba tare da bata lokaci ba suka samu nasara wajen hana gobarar yin barna mai yawa.
Guda daga cikin wadanda suka shaida faruwar tashin gobarar, Bilyaminu Musa Gwale, ya bayyana wa Freedom Radio musabbabin tashin gobara, inda ya ce, wani mai sayar da Shayi a kusa da gidan man ne ya zubar da Garwashi a daidai lokacin da ake tsaka da sauke man inda bayan ya zuba wutar a cikin kwata sakamakon cewa babu ruwa a kwatar sai kawai wutar ta tashi.
Ya kara da cewa, a nan ne suka yi gaggawar yin amfani da hodar kashe gobara wadda aka tanada a gidan man suka fara kashe wutar.
Haka kuma Bilyaminu Musa Gwale, ya tabbatar da cewa, babu asarar rai ko jikkata sakamakon gobarar, kana wutar ba ta yi wata babbar barna ba.
You must be logged in to post a comment Login