Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: An yi garkuwa da amarya kwana guda kafin ɗaurin aure

Published

on

Rahotanni daga unguwar Ƙoƙi da ke nan Kano na cewa an yi garkuwa da wata amarya da ake shirin ɗaura auren ta a ranar Lahadi 14-03-2021.

Ana zargin an yi garkuwa da budurwar mai suna Amina Gwani Shamwin Ɗan Zarga yayin da take hanyar dawowa gida daga unguwar Ɗorayi.

Ɗan uwan mahaifin ta Gwani Rayyanu Ɗan Zarga ya shaida wa Freedom Radio cewa, an kira su da wayar ta inda aka yi musu kashedi cewa kada su ƙara kiran wayar.

Sannan an aiko da saƙon kar-ta-kwana ga ƙanin ta, inda aka ce a taimaka mata da addu’a, saboda an kashe wadda suke tare a lokacin.

Ya ci gaba da cewa, a ranar Lahadi ake shirin ɗaura auren ta da saurayin da take so ta kuma gabata da shi ga iyayen ta, kuma babu wani saɓani a tsakani.

Mun tuntuɓi mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa sai dai ya ce, bai samu rahoton faruwar lamarin ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!