Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Budurwa ta aike wa saurayinta ƴan fashi

Published

on

Kotun majistiri mai lamba 18 da ke gyaɗi-gyaɗi a Kano ta ƙi amincewa da bada belin budurwar da ta aika wa saurayinta ƴan fashi.

A zaman kotun na ranar Alhamis mai shari’a Auwal Yusuf Sulaiman yayi watsi da buƙatar lauyoyinta inda suka nemi a bada belinta da matasan da ake zargin ta aika don afka wa saurayinta.

A kwanakin baya ne aka zargi budurwar mai suna Fatima Umar mazauniyar Ɗantsinke da ke ƙaramar hukumar Kumbotso da aika wa saurayinta gungun wasu matasa 6 har gida ɗauke da makamai saboda ya daina son ta.

Mai shari’a ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 30 ga watan Disamban da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!