Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zafin Kishi: Uwargida ta sara kan kishiyarta da adda

Published

on

Gwamnatin Kano ta gurfanar da wata mata mai suna Fatima Ɗahiru mazauniyar Hotoro a babbar kotun jiha mai lamba biyu da ke sakatariyar Audu Baƙo, ƙarƙashin mai shari’a Aisha Rabi’u Ɗanlami.

Ana zargin Fatiman da sarawa kishiyarta adda a tsakiyar ka, inda kanta ya rabe gida biyu, lamarin da yayi sanadiyyar rasa ranta.

Yayin zaman kotun na ranar Alhamis wadda ake zargin ta musanta.

Sai dai lauyan gwamnati Barista Lamiɗo Abba Soronɗinki ya gabatar da shaidu huɗu, sai dai kotu ba ta ƙarɓi shaidun ba, saboda lauyan da ke kare matar ya rasu.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar har zuwa ranar 13 ga watan Janairu mai kamawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!