Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Ganduje ya haramta ɗaga allunan siyasa yayin bikin Sallah

Published

on

Gwamnatin Kano ta haramta liƙa hotuna da ɗaga tutucin siyasa a lokacin bukukuwan ƙaramar Sallah.

Hakan na cikin saƙon sallah da Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fitar, ta hannun Kwamishinan yaɗa labara na jiha Malam Muhammad Garba.

Gwamna ya ce, daga yanzu an hana sanya tutoci, ko allunan ƴan siyasa yayin sallar idi da sauran taruka na bukukuwan sallah domin kaucewa rikici.

Ya ce, Sallar idi ibada ce muhimmiya bayan azumin Ramadana da ake bin bayanta da bukukuwan bajakolin tarihi da al’adu, wanda ake zuwa kallo har daga ƙasashen ƙetare.

Saboda haka bai kamata a mayar da waɗannan wurare wajen gangamin siyasa da yaƙin neman zaɓe ba.

Gwamna ya jaddada cewa, ɗaga allunan siyasa a yayin taron da ya haɗa jama’a masu mabanbantan ra’ayi kamar Hawan Daushe, ka iya haifar da tarzoma.

Sanarwar ta kuma umarci ƴan siyasa da su tabbatar sun yi biyayya sau da ƙafa ga sabuwar dokar zaɓe.

Gwamna Ganduje ya taya al’ummar musulmi murnar bikin Sallah, tare da fatan za su yi riƙo da abin da suka koya a watan azumi.

Sannan ya yi kira ga jami’an tsaro da su nuna halin ba sani ba sabo, ga duk wanda yayi ƙoƙarin tayar da tarzoma yayin bukukuwan sallar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!