Labarai
Kano: Gini ya rufto kan mutanen da suka fake wa ruwan sama

Wani ginin bene mai hawa 4 da ba a kammala ba a kan titin Abeadi da ke unguwar Sabon Gari a Kano ya rufto tare da danne wasu mutane waɗanda suka fake wa ruwan sama.
Wani shaidar gani da ido ya tabbatar wa da manema labarai cewa, lamarin ya faru ne da yammacin Ranar Lahadi.
Ya ce, zuwa karfe 9 na dare an zaƙulo mutane 8 waɗanda aka garzaya da su asibiti cikin mawuyacin hali.
Hakan kuma, ya kara da cewa, Sai dai masu aikin ceto sun dakata sakamakon dare da rashin samun motar da za ta yi aikin janye ɓaraguzan ginin.
You must be logged in to post a comment Login