Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Marka-markar ruwan sama ta yi sanadiyyar rasa rai a Kano

Published

on

Rushewar gida ta jikkata mutane uku tare da rasa ran yaro ɗaya a unguwar ƙofar Kansakali layin Alhawali da ke ƙaramar hukumar Gwale a nan Kano.

Lamarin ya faru ne da asubahin yau Talata sakamakon ruwan sama da iska da aka tafka, inda gidan wani Magidanci mai suna Alhaji Umar Baba ya ruso a kan ƴaƴansa, kuma a lokacin da magidancin ya je don ganin abin da ya faru sai ginin ya ƙara ruftawa da shi.

Mai ɗakin magidancin Aisha Umar ta shaidawa Freedom Radio cewa mai gidan ta da ƴaƴanta biyu suna asibiti ana ci gaba da duba lafiyarsu, bayan da maƙota suka kawo musu ɗauki.

Sai dai, ɗanta guda ɗaya Muhammad Umar ɗan shekara 12 ya rasa ransa.

Wani daga cikin maƙota da suka kai musu ɗauki mai suna Muhammad Ibrahim ya shaida wa Freedom Radio cewa, ya fito zuwa masallaci kawai sai ya ji ƙarar faɗuwar ginin wanda hakan ya sanya ya gayyato al’umma suka kawo musu ɗauki.

Hukumar kashe gobara ta Kano ta tabbatar da faruwar al’amarin kamar yadda kakakinta Sa’idu Muhammad Sule ya tabbatar wa Freedom Radio.

Sa’idu Sule ya kuma nemi al’umma da su riƙa ɗaukar mataki a duk lokacin da suka lura da gini ya fara nuna alamun zaftarewa.

*BS*

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!