Labarai
Kano: Hisbah ta cafke matar da ake zargi da bai wa matasa mafakar aikata Baɗala

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta kama wata mata da ake zargi da tara matasa a gidanta domin aikata badala a yanki Hotoro Walawai da ke Ƙaramar hukumar Taruani.
Wannan dai na zuwa ne bayan korafe-korafen al’ummar yankin kan wadanda ake zargin.
Mutane 11 da hukumar ta kama sun hadar da maza 4 da kuma mata 7.
Mataimakin babban Kwamandan hukumar ta Hisbah Dakta Muhajiddin Aminuddin, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.
Matar da ake zargi da bayar da mafaka ga masu aikata laifin mai suna Aisha yar asalin jihar Adamawa da kuma wadanda aka kama yayin sumamen da Hisbah ta kai, sun bayyana nadamarsu bayan sun shiga hannu.
Haka kuma mataimakin babban Kwamandan hukumar ta Hisbah Dakta Muhajiddin Aminuddin ya bukaci al’umma da su ci gaa da bai wa hukumarsu hadin kai wajen yaki da aikata laifuka.
You must be logged in to post a comment Login