Labarai
Kano: Hisbah ta kama matasa 5 bisa zargin shirya aure ba bisa ka’ida ba

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu matasa maza da mata su biyar bisa zargin gudanar da bikin aure ba tare da amincewar iyaye ko bin ka’idojin aure na Musulunci ba.
Mataimakin kwamandan hukumar ta Hisbah, Dakta Mujaheedden Aminuddeen, ne ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’ansu sun dauki matakin ne bayan rahotannin da mazauna yankin da aka shirya auren suka bayar.
Haka kuma, Dakta Mujahiddin Aminuddeen ya bayyana cewa wannan aure ya saba wa koyarwar addinin Musulunci da dokokin jihar Kano.
Ya kuma bayyana cewa, hukumar za ta ci gaba da daukar mataki kan duk wanda ya yi aure ba bisa doka ba.
You must be logged in to post a comment Login