Labarai
Kano: Hukumar KAROTA ta kai sumame wajen boye magunguna
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA karkashin jagorancin shugabanta Baffa Babba Dan’agundi, ta samu nasarar kame wasu manyan kata-katan guda 28 na wasu magunguna da aka shigoda su jihar Kano wadanda basu da lambar hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa watau NAFDAC.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya raba wa manema labarai yau Alhamis 30 ga watan Janairu 2020.
Sanarwar ta ce hukumar ta kama magungunan ne a wani wurin ajiye magunguna da ke titin zuwa filin jirgin saman Malam Aminu Kano wani sumame da kwararrun jami’anta suka kai wurin domin gudanar da bincike bisa zargin shigo da magunguna ta barauniyar hanya ana boye su.
Hukumar ta ce kasancewar ta daya daga cikin kwamitin kar ta kwana da gwamnatin jihar Kano ta kafa domin yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi da hana yaduwarsu cikin al’umma ya sanya hukumar ta kai sumame wurin a jiya laraba domin gudanar da bincike.
Ta cikin sanarwar dai, shugaban hukumar Baffa Babba Dan’agundi ya bayyana cewa hukumar za ta yi dukkan mai yiwuwa tare da amfani da damar da doka ta bata wajen ganin ta kiyaye dokoki da rage aikata laifuka a titinan jihar Kano.