Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Hukumar SERVICOM tayi sammacin wani darakta a Kano

Published

on

Hukumar kula da tabbatar da da’ar  ayyukan ma’aikata ta Kano SERVICOM tayi sammacin Babban Daraktan mulki na Ma’aikatar ciniki ta jihar Kano kan rashin zuwa aiki da wasu daga cikin ma’aikatan su domin yayiwa hukumar bayani kan lamarin.

Shugaban Hukumar ta Kano Tijjani Bello Abubakar ne ya bayyana hakan a yau lokacin daya jagoranci tawagar ma’aikatan Hukumar domin zagaya hukumomin gwamnati don ganin yadda al’amuran ma’aikatu ke wakana.

Tijjani Bello yace dalilin ziyarar tasu shine domin su gana da shugabannin hukumomin domin su sami bayanai daga gurinsu kan yadda za’a magance matsalolin ma’aikata tare da shaida musu matsalolin da suke fuskanta domin a gyara.

Shugaban Hukumar Tijjani Bello ya kuma yi kira ga sauran ma’aikata a fadin jihar Jihar Kano dasu kasance masu akidar zuwa guraren ayyukansu akan lokaci da kuma dai na fashin zuwa aiki don kuwa hukumar zata cigaba da daukar mataki akan marasa zuwa aiki.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito tawagar hukumar a yau ta ziyarci ma’aikatar kasuwanci ta jihar Kano da Ma’aikatar harkokin Gona da hukumar kula da Asibitoci ta Kano domin ganin yadda ayyukan ma’aikata ke gudana.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!