Labarai
Kano: Jigo a jam’iyyar APC ya zarge ta daƙile su

Wani jigo cikin tsaffin kansilolin jihar Kano da gwamna Abba Kabir Yusuf ya biyasu hakkokin su na sama da biliyan 8.
Ya soki jagororin jami’iyyar APC da yi musu bita da kulli na rashin biyansu hakkokinsu tun da wuri.
Malam Abdussalam Ishaq jigo a Jam’iyyar APC din karamar hukumar Kumbotso ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya raba ga manema labarai.
Haka kuma tsohon Kansilan, ya yaba wa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kokarin da ya yi wajan biyansu, duk kuwa da ba jami’iyyarsu daya ba.
You must be logged in to post a comment Login