Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

APC ta zargi gwamna Abba Kabir da yunkurin kwashe kudin kananan hukumomi

Published

on

Jam’iyyar APC a Kano ta zargi gwamnan  jihar Kano Abba Kabir Yusuf, da yunkurin kitsa yadda za’a kwashe kudaden kananan hukumomi sama da biliyan takwas domin gina sabuwar gada a Kofar Danagundi da Tal’udu, adaidai lokacin da ake dakon jiran hukuncin Kotun Kolin kasar nan.

Ta cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai.

Abdullahi Abbas ta cikin sanarwar ya gargadi majalisar kananan hukumomin Kano da sauran bankuna masu zaman kansu da kada su sanya kansu a wajen fitarda kudaden da za’ayi aikin dasu, musamman a wannan lokacin da jam’iyyar NNPP ta shiga cikin rudani dan gane da hukuncin da Kotun Koli zata yanke.

Shugaban jam’iyyar ta APC Abdullahi Abbas, yace a ranar Juma’ar data gabata gwamnatin Jihar Kano ta fitarda sanarwar nadin Daraktocin gudanarda harkokin mulki da Ma’aji na kananan hukumomi baki daya wanda hakan zai basu dama wajen ganin sun gudanarda yunkurin nasu nayin almubazzaranci da kudaden kananan hukumomin 44 ba tare da sun fuskanci wata matsala ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!