Labarai
Kano: Kotu ta daure masu gadi bayan samun su da sata

Kotun Majistiri mai lamba 2 da ke Gyadi-gyadi a Kano karkashin jagorancin mai shari’a Auwal Yusuf, ta yanke wa wasu masu gadi hukuncin zaman gidan gyaran hali bayan samun su da laifi.
Masu gadin sun hada da Dahiru Hassan da Mu’azzam Ali inda alkalin ya yanke musu hukuncin daurin watanni 6 ko kuma biyan tarar naira dubu ashiri a laifin hada kai wajen aikata laifi.
Haka kuma, kotun ta ce ta same su da aikata sata inda a kan laifin ta yi musu hukuncin daurin shekaru 2 ko biyan tarar naira dubu dari.
Kana kotun ta yanke musu hukuncin biyan kudin ramko har Naira miliyan biyu da dubu dari bakwai da hamsin ko zaman gidan gyaran hali na shekaru biyu.
Wani mutum Mai suna Abubakar Abban Sultan ya yi korafi cewa masu yi musu gadi sun satar musu kayayyaki, a wurin da suke yi musu gadi a kan titin Ibrahim Taiwo.
You must be logged in to post a comment Login