Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin kisa ga wani matashi

Published

on

Wata babbar kotun shari’ar musulnci dake zaman ta a Kano karkashin mai shari’ah Aliyu Muhammad Kani, ta yake hukuncin kisa ga wani matashi Yahaya Sharif Aminu Sharifai, bisa samun sa da laifin aikata batanci ga fiyayyen halitta manzo sallalahu alaihi wasallama, ta hanyar rubutu a wani group din WhatsApp.

Ka zalika wani matashi Umar Faruk Bashir dan unguwar Sharada, da shima kotun ta yankewa hukuncin shekaru goma tare da aiki mai tsanani  a gidan ajiya da gyaran hali, sakamakon samun sa da kotun ta yi da laifin aikata sabo ga Allah subahahu wata’ala, ta hanyar yin musu a majalisa.

Tun a baya dai dan sanda mai gabatar da kara a kotun Aminu Sani ‘Yar Goje, ya karanta musu kunshin tuhumar sun kuma amsa.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya ruwaito cewa, bayan an yanke hukuncin an danka masu laifin  a hannun jami’in gidan ajiya da gyaran hali, Yakubu Bala Jibrin bisa jagorancin mai magana da yawun su DSC Musbahu Lawan Kofar Mata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!