Connect with us

Labarai

Kano: Kotu ta sauke Basaf daga shugabancin Kumbotso tare da bai wa Ali Dan Maliki nasara

Published

on

Babbar kotun jihar Kano mai lanba 17 karkashin jagorancin mai sharia Abdu Maiwada Abubakar, ta bai wa hukumar zabe ta Kano  umarnin soke shaidar lashe zabe da ta bai wa Gali Shitu Basaf da ta bashi damar kasancewa shugaban karamar hukumar Kumbotso.

 

Haka kuma kotu ta  umarci a rantsar da Ali Musa Dan Maliki, a matsayin shugaban karamar hukumar ta Kumbotso.

 

Tun a baya dai, Ali Musa shi ne ya garzaya kotu ya ke kalubalantar rantsar da Gali Shitu Basaf a matsayin shugaban karamar hukumar.

 

Hakan ta sanya ya roki kotu da ta soke shaidar lashe zaben da hukumar zaben watau KANSIEC ta bai wa Gali Shitu Basaf.

 

Kotun dai ta amince ta soke shaidar lashe zaben inda ta kuma umarci a mayar wa Ali Musa kujerar.

 

Haka kuma kotun ta umarci gwamnati ta rika bin umarnin kotu da zarar ta yi hukunci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!