Labarai
Kano: Ma’aikatan wucin gadi na SEMA sun zargi hukumar da nuna musu wariya

Ma’aikatan wucin gadi a Hukumar Bada agajin gaggawa da kare Iftilai ta Jihar Kano SEMA sun gudanar da wani gangami a Gidan Gwamnatin Kano tare da mika korafin cewa Hukumar na nuna musu wariya wajen daukar ma’aikata.
Shugabar kungiyar ma’aikatan wucin gadin Rukayya Hassan, ta shaidawa wakilinmu Abba Isah Muhammad, cewar mambobinsu fiye da dari sun shafe shekaru masu yawa suna aikin sakai batare da daukar su a matsayin cikakkun ma’aikata ba.
Galibin ma’aikatan da suka gudanar da gangamin mata ne inda su ke fatan gwamna da hukumar ta SEMA za su duba koke nasu.
Sai dai shugaban Hukumar Bada agajin gaggawar ta Jihar Kano Isyaku Abdullahi Kubarachi, ya ce, akwai matakan karatu da ake dubawa kafin daukar ma’aikatan, kana za a ci gaba da dauka ba wai an kammala ba ne.
You must be logged in to post a comment Login