Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnati ta fara daukar ma’aikatan wucin gadi a Kaduna

Published

on

A jihar Kaduna, an fara daukar matasa su dubu ashirin da uku ayyuka na wucin gadi, ta cikin shirin nan na gwamnatin tarayya na daukar mutane dubu daidai a kowace karamar hukumar.

An dai fara ne a yau asabar, wanda ya gudana a Fatika da ke yankin karamar hukumar Giwa a jihar ta Kaduna, karkashin bin dokokin kariya daga kamuwa daga cutar corona.

Da take jawabi yayin bikin fara daukar ma’aikatan da ke karkashin ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi, shugabar kwamitin zabar ma’aikatan kuma kwamishiniyar ayyukan walwala da ci gaban al’umma na jihar, Hajiya Hafsat Baba, ta ce, shirin na daukar ma’aikatan da gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar yi guda dubu 774, 000 a jihohi 36 kasar zai taimaka gaya wajen rage zaman banza tsakanin matasa.

Hajiya Hafsat Baba ta kuma ce, za su yi iya kokarinsu wajen ganin matasan jihar sun amfana da shirin yadda ya kamata don magance matsalolin rashin aikin yi a tsakani matasa.

Ta kara da cewa, ‘yan siyasa a  jihar Kaduna za su samu kaso 13 na gurbin daukar ma’aikatan, yayin da kaso 87 za a duba matasan da suka cancanta karkashin kwamitin don basu damar morar shirin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!