Labarai
Kano: Ma’aikatar Muhalli ta yaba wa ƴan hidimar ƙasa bisa tsaftace Sakatariyar Audu Bako

Ma’aikatar Muhalli da sauyin yanayi ta Jihar Kano ta yaba da yadda matasa masu yiwa kasa hidima NYSC, a sakatariyar Audu Bako suka gudanar da gangamin tsaftar Muhalli a yau Asabar.
Kwamishinan Muhalli da sauyin yanayi Dakta Dahiru Muhammad Hashim, wanda ya samu wakilcin Daraktar wayar da kan jama’a Maryam Abdulkadir, ta bayyana wannan yabo, inda kuma ta yi kira ga matasan da su dore da tsaftace muhalli a duk inda suka samu kansu.
Da ya ke jawabi, daya daga cikin matasa ƴan hidimar ƙasa NYSC, ya bayyana dalilan da suka sanya su gudanar da gangamin tsaftar Muhallin.
Kimanin matasa yan hidimar ƙasa da ke a ma’aikatar muhallin su 17 ne suka gudanar gangamin a yau.
You must be logged in to post a comment Login