Labarai
Kano: Ma’aikatar Sufuri ta kafa kwamitin inganta ayyukanta

Ma’aikatar Sufuri ta Jihar Kano, ta kafa kwamiti na musamman domin ingantawa da tabbatar da tsarin aiki mai ɗorewa a ma’aikatar.
Wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnati na inganta ayyukan ma’aikatar domin cimma nasarorin da ake bukata a fannin na sufuri.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ma’aikatar Zaharaddeen Adam Ibrahim Gora, ya fitar a daren jiya Litinin.
Sanarwar ta ruwaito cewa, yayin taron ƙaddamar da kwamitin, Kwamishinan Sufuri na Kano Barista Haruna Isah Dederi ya buƙaci dukkan jami’ai da shugabannin ma’aikatar da su hada kai tare da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ta na da cikakkiyar niyyar tabbatar da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta wajen samar da ingantattun ayyuka da kyakkyawar kulawa ga al’ummar jihar Kano.
Kwamishinan, ya yaba da irin jajircewar jami’an ma’aikatar tasa tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa musu wajen sauke nauyin da ke kansu, domin ci gaban Jihar Kano baki ɗaya.
A nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatar, Alhaji Abdulmumin Musa Aliyu, ya bayyana cewa an shirya tsarin kwamitin ne domin tabbatar da hadin kai tsakanin sassan daban-daban na ma’aikatar, tare da inganta gudanar da ayyukan yau da kullum cikin inganci da gaskiya.
You must be logged in to post a comment Login