Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Matasa sun yi rabon kayan tallafi ga asibitoci

Published

on

Ƙungiyar matasan mazaɓar Hotoro NNPC, ta miƙa kayan tallafin kiwon lafiya ga wasu asibitoci uku da ke yankin.

Shugaban ƙungiyar Kwamared Jamilu Magaji Saleh Hotoro ne ya jagoranci miƙa tallafin a ranar Laraba.

Kwamared Jamilu ya ce, sun bada tallafin ne duba da halin da asibitocin ke ciki, na rashin kayayyakin aiki.

Da yake jawabi yayin miƙa tallafin Dagacin Hotoro Walawai Alhaji Mustapha Abubakar, ya bayyana farin cikinsa, sannan ya hori ma’aikatan asibitocin da su yi aiki da kayayyakin yadda ya dace.

Asibitocin da suka samu tallafin sun haɗar da, asibitin Hafizu Kawu da ke Hotoro Walawai da asibitin Tsamiyar Boka da kuma na Mai Tuwo.

Dukkan asibitocin suna yankin ƙananan hukumomin Tarauni da Nassarawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!