Labarai
Kano: Mutane fiye da 1,000 da ake zargi da ayyukan Daba sun ajiye makamansu

Rundunar ’yan sanda ta jihar Kano ta ce zuwa yanzu, kimanin mutane sama da dubu daya da ake zargi da faɗan daba ne suka ajiye makamansu a shalkwatar hukumar da ke Bampai.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yi wa wakilinmu Abba Isah Yakasai ƙarin haske, kan matakan da suke ci gaba da dauka na dakile miyagun laifuka.
SP Kiyawa, ya kuma yi gargadi ga matasan da ke cigaba da bidiyo da ke nuna ayyukan daba ko rike makamai a shafukan sada zamunta.
You must be logged in to post a comment Login