Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Yan sanda sun gurfanar da matasa 104 da ake zargi da ayyukan Daba

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta gurfanar da matasa 104 da ake zargin yan Daba ne a gaban wasu kotuna da ke unguwar Nomandsland.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a sahihin shafinsa na Facebook.

SP Kiyawa, ya kara da cewa ana zargin mutanen da laifukan Daba da riƙe makamai da kuma tu’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Haka kuma, ya ce sun gurfanar da mutanen ne bayan binciken da aka yi a sashen binciken manyan laifuka na rundunar kamar yadda kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel ya umarta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!