Connect with us

Labarai

Kano na iya fuskantar barazanar zaizayar kasa-NEWMAP

Published

on

Shirin kare zaizayar kasa da alkinta albarkatun ruwa na NEWMAP ya ce, kowane bangare na jihar Kano na fuskantar matsalar zaizayar kasa sakamakon yawaitar tone kasar gini barkatakai da kuma toshe magudanan ruwa.

Shugaban kula da shirin a nan jihar Kano, Malam Musa Shuaibu ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan Freedom Radio.

Ya ce, akwai wurare da dama na jihar Kano da suke fuskantar wannan matsala ta zaizayar kasa.

Ya kuma ce, babban abinda ke haifar da toshewar magudanan ruwa a wasu wurare baya rasa nasaba da yadda wasu daga cikin al’umma ke zuba shara a cikin magudanan ruwa barkatai.

Shugaban kula da shirin na NEWMAP ya kuma ce za su ci gaba da wayar da kan al’umma game da illar wannan dabi’a da ke janyo barazana ga muhalli a jihar Kano da ma kasa baki daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!