Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukuncin kotu kan sakin Sanusi II

Published

on

Wata babbar kotu a birnin tarayya Abuja, yau jumma’a  ta bada umarnin a gaggauta sakin tsohon sarkin Kano Malam Muhammadu  Sunusi, da aka tura garin Awe, dake jihar Nassarwa.

Mai sharia’a Anwuli Chikere, ya bada umarnin bayan da mai shigar da kara   Lateef Fagbemi, mai mukamin (SAN), ya nema.

Mai  shari’a  Chikere, ya kuma umarci da a  gaggauta  sakin  tsohon sarkin ba tare da wani bata lokaci ko gindaya wasu sharuda ba.

Karar  da tsohon sarkin ya shigar ta hada da babban sufeton ‘yan sanda na kasa, Muhammed Adamu; sai shugaban hukumar jami’an tsaro na farin kaya  DSS, Yusuf Bichi; babban mai shari’a ministan sharia’a na kasa Abubakar Malami, da  kwamishinan sharia’a na jihar Kano, Ibrahim Muktar, wand sarkin ya zarge su da hannu wajen tsare shi ba bisa doka ba.

Mai shari’a Anwuli Chikere, ya sanya ranar 26 ga watan Maris din da muke ciki don cigaba da saurarar karar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!