Labarai
Kano: NDLEA ta cafke wani matashi da kwayoyin Tramadol guda 7,000

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA shiyyar Kano, ta ce, ta samu nasarar kama wani matashi da ya ke kokarin shigo wa Kano daga jihar Lagos da kwayoyin Tramadol da suka kai adadin guda dubu bakwai.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sakon Murya da mai Magana da yawunta Sadik Muhammad Maigatari ya fitar.
Ya ce, sun kama matashin ne mai suna Adamu Yusuf a kwanar Dangoro da ke kan Titin zuwa Zaria.
Haka kuma ya kara da cewa sun cafke matashin ne a ranar 23 ga wannan watan da muke ciki na Agusta, dauke da kwayoyin na Tramadol masu nauyin Kilo giram 4.1.
You must be logged in to post a comment Login