Labarai
Kano Pillars ta musanta wasu zarge-zarge da ake yaɗa wa kan ƙungiyar

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta musanta wasu zarge-zargen da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta dangane da jagororin tawagar.
A cewar ƙungiyar wasu marasa kishin jihar Kano da harkokin wasanni su ke ɗaukar nauyin yin hakan.
Ta cikin sanarwar da sashen yaɗa labarai na kungiyar ya fitar, Kano Pillars ta yi kira ga magoya bayan tawagar da su yi watsi da irin waɗannan kalami da ta kira da karairayi.
Haka kuma ta ƙara da cewa babu ƙamshin gaskiya a cikin irin waɗannan labarai.
You must be logged in to post a comment Login