Connect with us

Labaran Wasanni

Kano Pillars ta nada sabon mai horas wa

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nada Mr. Lione Emmanuel Soccia a matsayin sabon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Shugaban kungiyar Alhaji Surajo Sha’aibu Yahaya Jambul ne ya bayyana hakan, inda ya ce gwamna Ganduje ya bada umarnin ganin cewa Kano Pillars ta cika dukkanin ka’idojin da hukumar kwallon kafa ta Afrika ta tanada a gasar cin kofin kalubale.

Mr. Emmanuel Soccia dai dan kasar Faransa ne, kuma zai jagoranci Kano Pillars a gasar cin kofin na kalubale na shekara 2020/2021.

Jami’in yadda labaran kungiyar Rilwanu Idris Malikawa, ya ce yanzu haka sabon mai horas war yana a kasar nan, yayin da za a kuma a kaddamar dashi a gobe Labara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!