Labarai
Kano Pillars ta sha alwashin ɗauka ƙara kan hukuncin kwamitin NPFL

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta ce zata dauka kara, kan hukuncin da kwamitin shirya gasar cin kofin Firimiya ta Najeriya NPFL ya dauka a kanta na rage mata maki uku da kwallaye uku kuma cin tararta naira miliyan Tara da dubu dari biyar
Kana da hukuncin haramta mata buga wasanninta na gida a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata, sakamakon yadda magoya bayanta suka tayar da tarzoma bayan tashi daga wasan mako na takwas tsakaninta da Shooting Stars.
Wannan lamari ya faru ne a ranar Lahdi da ta gabata inda suka buga wasan da aka tashi kunnen doki da ci 1-1.
You must be logged in to post a comment Login