Labarai
Kano: Wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun shiga Garin Gulu

Mazauna garin Gulu da ke yankin ƙaramar hukumar Rimin Gado, sun buƙaci hukumomin tsaro da su gaggauta kai musu dauki, sakamakon yadda ’yan bindiga suka fara kai hari a yankin.
Rahotonni sun bayyana cewa, da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Alhamis wasu ƴan bindiga dauke da makamai suka shigo cikin garin tare da yin harbe-harbe don razana mazauna yankin.
A wata tattaunawar da Freedom Radio ta yi ta wayar tarho da Malam Abba Rabi’u Gulu, mazaunin garin, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, sun kai harin ne wani kanti inda suka kwaci kuɗi da kayan masarufi.
Haka kuma ya ƙara da cewa, ɓata garin sun ƙwace wa wata matashiya Waya bayan da suka raunata ta.
Malam Abba ya tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa, kuma babu wanda aka yi garkuwa da shi, sai dai fargaba da tashin hankali da harin ya haifar wa al’umma Garin.
You must be logged in to post a comment Login