Labaran Kano
Kano: ‘Yan kasuwa sun koka
Wani ‘dan kasuwa a nan Kano ya koka bisa rufe iyakokin Najeriya da gwamnatin tarayya ta yi, inda ya ce adadin mutanen da ke samun na kansu a dalilin shigo da kayayyaki ta iyakokin kasar nan sun kai kimanin mutane 100,000.
Shugaban rukunin kantunan Garba Karfe Alhaji Abba Garba, ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio, da ya mayar da hankali kan matsalolin da ‘yan kasuwa ke fuskanta sakamakon rufe iyakokin kasar nan, na kan tudu.
Alhaji Abba Garba ya kuma bayyana cewa za su yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin sun zauna da masu ruwa da tsaki wajen samun mafita ta yadda wadanda suka rasa sana’o’in su sakamakon rufe iyakokin za su cigaba da ayyukannsu.
A nasa bangaren shugaban kungiyar matasa ‘yan kasuwa na arewacin Najeriya Alhaji Abubakar Kabir, cewa ya yi kasuwanci a yanzu ya lalace sakamakon rufe iyakokin, har ma ya bukaci gwamnati kan ta saurari bukatun ‘yan kasuwar Najeriya, domin ganin an magance matsalar fatara da talauci da ake ciki.
Ya kuma ce yana da kyau gwamnati ta cigaba da kokarin da take yi wajen ganin an samu ci gaba a bangaren bunkasa tattalin arzikin Najeriya.