Connect with us

Labaran Kano

Zakin gidan Zoo ya kara bacewa

Published

on

Kai tsaye: Har yanzu ba’a kama Zakin da ya kubuce ba

Rahotonni daga gidan adana namun daji na nan Kano na cewa zakin nan da ya kubuce a jiya ya kara guduwa daga cikin kejin jiminar da yake ciki tun da rana.

Kakakin hukumar ta jihar Kano Hadiyatullahi Garba ya tabbatar mana da cewa sinadaran da kwararru suka taho dasu daga Abuja ba suyi amfani ba, domin kuwa sinadarai ne irin wanda mahukuntan gidan suke dashi, da su kayi amfani dashi tun da safe amma hakan su bai cimma ruwa ba.

Kakakin ya kara da cewa an yanke hukuncin a budewa Zakin wuta, amma koda aka yi masa harbi guda daya sai ya arce.

Inda ya garzaya cikin dajin dake gidan Zoo din.

A yanzu haka dai jami’ai na cigaba da neman Zakin ruwa a jallo domin har beshi har lahira.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,922 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!