Labarai
Kano: Yan sanda sun kama mutane 6 bisa zargin satar Adaidaita sahu da babura masu kafa 2

Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta kama mutane shida bisa zargin satar baburan adai-daita sahu da babura masu kafa biyu, tare da kwato wasu daga cikinsu.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya wallafa a shafinsa na Facebook.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce, a ranar 14 ga watan nan da muke ciki na Oktoba ne, jami’an yan sanda suka kama wasu mutane biyu wadanda suka yi yunkurin kwace wa wani matashi Adaidaita Sahu a kan titin zuwa filin jirgin sama bayan da suka bai wa matashi lemo wanda ya sanya shi fita daga hayyacinsa bayan ya sha.
Haka kuma a bayyana cewa zuwa yanzu sun gano baburan Adaidaita Sahu guda 3 da kuma babura masu kafa biyu guda 5.
You must be logged in to post a comment Login