Labarai
Kano: Yan sanda sun tabbatar da kama matashin da ake zargi da kashe Kakanninsa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbadar da tsare matashin nan da ake zargi da kashe kakanninsa ta hanyar caccaka musu wuka a unguwar Kofar Dawanau da ke Kano.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren ranar Al’hamis.
SP Kiyawa, ya kuma ce, da zarar an kammala gudanar da bincike kan wanda ake zargin za su gurfanar da shi a gaban kotu domin daukar mataki na gaba.
You must be logged in to post a comment Login