Labarai
Kano: Yan sanda sun tabbatar da mutuwar Baba-Beru

Rundinar yan sandan Kano ta tattabatar da mutuwar wani matashi Halifa wanda aka fi sani da Baba Beru wanda ake zarginsa da addabar unguwar Gwammaja da kewaye.
Jami’in hulda da jama’a na rundinar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da mutuwar tasa a ta cikin wani sakon murya da ya aikowa Freedom radio.
Kiyawa, ya cem a jiya Talata ne suka samu kiran gaggawa inda aka sanar da su cewa, wanda ya rana ran nasa tare da sauran wasu bata gari sun kai farmaki unguwar Gwammaja, inda bayan isar yan sanda ne suka yi artabu da su da ya kai ga faunatar jami’ain ‘yan sanda biyu tare da matashin Halifa, kuma bayan kai shi asibiti ne aka tabbatar da rasuarsa.
Haka kuma, ta cikin sanarwar, SP Kiyawa ya bukaci mutane da su rika kai rahoton duk wasu bata gari da ke addabar yankunansu.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya kuma ce rundinar za ta ci gaba da yin aiki tukuru domin tabbatar da ta kakkabe ayyukan fadace fadacan daba a fadin jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login