Labarai
Kano: Yara 2 sun rasu sakamakon nutsewa a Kwalbati

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar yara biyu sakamakon nutsewa a wata Kwalbati da ke garin Hayin Yawa Gada da ke yankin ƙaramar hukumar Tudun Wada ta Jihar Kano.
Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa, lamarin ya faru ne ranar Alhamis, da misalin ƙarfe biyu na rana, inda yara biyu, Habu Sani da Haruna Isah, masu shekara 15 suka shiga wanka Kwalbatin da ke kusa da gada, inda suka nutse abin da ya janyo suka rasa ransu.
Hukumar ta yi kira ga iyaye da al’umma da su tsawatar wa yara kada su kusanci wuraren da ruwa ke taruwa, don kauce wa irin wannan mummunan lamari.
You must be logged in to post a comment Login