Labarai
Kano9: Abubuwan da suka faru kan yaran Kano da aka sace cikin shekara guda
A ranar 11 ga watan Octoba na shekarar 2019 ne, kwamishinan yan sandan Kano na wancan lokaci Ahmed Iliyasu ya kira wani taron manema labarai, wanda ya sanar da cewar sun samu nasarar ceto wasu kananan yara 9 da ake zargin an sace daga Kano zuwa jihar Anambra.
Jim kadan bayan kammala taron manema labaran kwamishinan ya yiwa Freedom Radio karin haske.
Galibi dai wadannan yara basa jin hausa sanadiyyar jimawa da sukayi a hannun wadanda suka sace su, ga dai Farouk wanda aka canjawa suna zuwa Emma Abioka.
Daga cikin yaran akwai Usman Muhammad dan kimanin shekaru biyar wanda ko sunansa baya iya fada cikakke, amma ya iya karanta alkur’ani mai girma.
To ko yaya iyayen yaran suka ji lokacin da suka yi arba da ‘ya’yansu?
Bayan ‘yan kwanaki da wannan lamari, binciken likitoci ya nuna cewa an yi lalata da wasu daga cikin yaran, kamar yadda daya cikin likitocin da suka duba su ya bayyana, a gidan talabijin na gwamnatin Kano wato ARTV.
Yan sanda sun ci gaba da fadada bincike kan lamarin, inda suka kara gano wasu yaran da aka sace, harma suka yi shela ga iyaye cewa duk wanda dansa ya bata ya garzayo shalkwatarsu dake Bompai, domin dubawa daga ciki, kuma a wannan lokaci wakilinmu Abba Isah Muhammad ya samu zantawa da wasu iyayen da suka da ce.
To sai dai iyayen da aka taba sacewa yara, sun ci gaba da bayyana har ma suka kafa kungiya wadda ta yi ikrarin cewa sama da yara 300 ne suka yi layar zana a Kano wadanda har zuwa yanzu ba a kai ga gano su ba.
A bangaren gwamnatin Kano dai ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa don daukar mataki kan wadanda ake zargin, lamarin da ya sanya gwamna Abdullahi Umar Ganduje kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin tun daga tushe.
Kwamitin dai ya yi aikin sa a matakin farko tare da gabatar da rahotonsa ga gwamnatin, daga nan kuma gwamna Ganduje ya kara sahalewa kwamitin kan ya aiwatar da shawarwarin da ya bayar.
Mai shari’a Wada Umar Rano shi ne shugaban kwamitin, kuma wakilinmu Nasir Salisu Zango ya tambaye shi, ko ina aka kwana game da aikin su?
Tun a baya dai rundunar yan sandan Kano, ta ce ta gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, koda ya ke wasu rahotanni sun ce daya daga cikinsu ta arce daga gidan gyaran hali, kafin daga bisani jami’an tsaro su sake yi mata kofar rago.
DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne jami’in hurda da jama’a na rundunar yan sandan Kano, ya yi min karin haske kan inda suka kwana game da lamarin.
Ku kalli hotuna lokacin da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa na yaran da wadanda ake zargi a shafin Facebook.
Batun sace yaran dai ya dauki hankalin al’umma da dama a ciki da wajen kasar nan, inda kafafen sada zumunta suka cika da sakonni, na ayi adalci ga yaran Kano 9, ko kuma ayi adalci ga mutanen Kano da makamantansu.
Irin wannan dai ya taba faruwa a baya inda aka samu wata budurwa yar kabilar ibo da ta biyo saurayinta zuwa jihar Kano da zummar suyi aure, wanda daga karshe abin ya rikide har aka mika shi hannun mahukuntan wata jihar a Kudu.
You must be logged in to post a comment Login