Labarai
KANO:PDP ta yi barazanar shigar da kara kotu don kalubalantar sakamakon zabe
Jam’iyyar PDP dake nan Kano ta yi baranzanar shigar da kara a gaban kotu, don kalubalantar sakamakon zaben gwamnan da aka yi a wasu daga cikin mazabu dake nan Kano.
Jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa an tafka magudi da kuma kura-kurai a yayin zaben da bai kammala wanda aka yi a shekaran jiya Absabar 23 ga wannan watan.
Mai rikon mukamin shugaban jam’iyyar dake nan Kano Rabiu Suleman Bichi ya sanar da hakan a yayin da yake ganawa da manema labarai anan Kano cewa, tun da fari sun gabatarwa hukumar zabe dake nan Kano korafe-korafen su kan cewa ba su gamasu da yadda aka yi zaben ba, tun kafin a sanar da sakamakon zaben.
Yayin da Jagoran jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas ya ce ya gamsu da yadda zaben ya gudana yana mai cewa ya godewa All… da sakamakon.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC it ace ta sanya ranar 23 ga wannan watan don gudanar da zaben da ba’a kammala ba, a jihohin Sokoto da Bauchi da Filato da kuma nan Kano.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewar jam’iyyar PDP taki amincewa da sakamakon zaben a wadannan jihohin, tana mai zargin cewa a tafka magudi a yayin zabukan da ba’a kammala ba.