Labarai
Kansilolin Kano sun buƙaci mutane su tabbatar sun mallaki katin zaɓe

Gamayyar kungiyoyin Kansilolin jihar Kano na ƙananan hukumomi 44, sun buƙaci mutane da su tabbatar da cewa, sun fito domin yin rijistar katin zaɓe saboda da shi ne kadai za su iya kawo sauyin da ake bukata a Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
Shugaban ƙungiyar Bashir Shehu Achika, ne ya bukaci hakan yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar ta gudanar.
Bashir Shehu Achika, ya kuma yaba wa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf kan yadda ya bai wa Kansilolidamar samar da ayyuakan more rayuwa ga al’ummar su.
You must be logged in to post a comment Login