Coronavirus
Karɓar rigakafin Covid-19 zai takaita yaɗuwar ta – FRI

Gidan Rediyon Manoma na Duniya wato Farm Radio International ya shawarci al’umma da su karɓi rigakafin Covid-19 domin taƙaita yaɗuwar ta
Gidan Radiyon na yin gargaɗin ne daidai lokacin da annobar corona samfurin Omicron da IHU ke ci gaba da bazuwa a wasu ƙasashen duniya.
A cewar FRI yin rigakafin ita ce hanya ɗaya da a daƙile ci gaba da bazuwarta a ko’ina a faɗin duniya.
Sannan ta gargaɗi mutane da su guji mallakar shaidar rigakafin ta bogi.
You must be logged in to post a comment Login