Labarai
Karancin abinci: za a samar da hukumar kula da Abinci ta kasa
Majalisar dattijai ta zartar da wani kudiri da ke neman kafa hukumar kula da Abinci ta Kasa.
Wannan ya biyo bayan nazari da kuma amincewa da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan Noma da raya Karkara.
Shugaban kwamitin, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce samar da hukumar zai aiwatar da manufofin hukumar kula da Abinci ta Kasa baki daya don tabbatar da samar da ingantaccen kayan masarufi a kasar nan.
Ya ce, karkashin hukumar ne za ta magance matsalolin da ake fuskanta na karancin abinci musamman lokacin da aka fada yanayi na annoba.
Sai dai kafin a zartar da kudurin, kan ‘yan majalisar ya rarrabu kan yiwuwar kafa hukumar.
You must be logged in to post a comment Login