Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Dan tsami: Mutane 10 sun mutu a Kano an kwantar da 400 a asibiti

Published

on

Gwamnantin jihar Kano ta ce akalla mutane goma ne suka mutu yayin da wasu dari hudu suke ci gaba da karbar magani a asibiti sakamakon shan lemo da ke dauke da sinadarin dan tsami.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana haka ta cikin wani faifan bidiyo da aka rabawa manema labarai yau anan Kano.

Ya ce, cikin wadanda suke karbar magani a asibitin, akwai wasu guda hamsin wadanda suka kamu da ciwon hanta.

Kwamishinan ya kuma shawarci jama’a da su guji amfani da sinadarin dan tsami a wannan lokaci na azumi, domin gudun ta’ammali da wanda ya gurba ce.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!