Labarai
Karancin man fetur ka iya shafar zaben 2023-INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya INEC ta ce karancin man fetur da ake fama da shi a kasar ka iya shafar shirye-shiryen gudanar da zabukan da za a yi a ranakun 25 ga watan Fabrairun da muke ciki da kuma 11 ga Maris.
Shugaban hukumar na kasa Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a Abuja a wani taron tuntubar juna da kungiyoyin sufuri irinsu NARTO da NURTW da dai sauransu.
Wanda ya ce, ‘abin damuwa ne matuka game da halin da ake ciki na karancin man fetur a kasar, da kuma tsadarsa wanda hakan yake shafar harkokin sufuri, kuma zai iya shafar sufurin a lokacin zabe. ‘
‘hukumar INEC za ta gana da kamfanin man fetur na kasa NNPC a yammacin yau Laraba domin duba hanyoyin da za a bi don magance matsalar. ‘
Rahoton: Madeena Shehu Hausawa.
You must be logged in to post a comment Login