Connect with us

Kaduna

Karin dalibai 10 na makarantar Bathel Baptist sun shaki iskar ‘yanci bayan sace su

Published

on

Karin wasu dalibai 10 da aka sace na makaranatr Bethel Baptist, ta karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, sun shaki iskar ‘yanci.

Shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa reshen jihar Kaduna, Rabaran John Hayab, ne ya tabbatar da sakin daliban ga manema labarai ranar Lahadi a Kaduna, inda yace ya zuwa yanzu adadin daliban da aka sako ya kai 110.

A ranar 5 ga watan Yulin da ya gabata ne, ‘yan bindiga suka mamaye makarantar tare da yin garkuwa da dalibai 121.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da sakin daliban 10.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!